Dan majalisar tarayya na Tarauni da Tirabunal ta kora ya ci alwashin ɗaukaka ƙara

 


Mukthar Umar Zakari (NNPP-Kano) ya sha alwashin kalubalantar hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke wanda ta soke zaben sa kan zargin amfani da takardun makaranta na bogi.

Zakari, wanda aka fi sani da Yarima, shi ne wakilin mazabar Tarauni a majalisar tarayya, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya rawaito cewa, kotun ta soke zabensa tare da bayyana Hafizu Kawu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Kwamitin mutum uku na kotun, karkashin jagorancin mai shari’a I.P. Chima, ya yanke hukuncin cewa bai cancanci tsayawa takara ba bayan ya yi amfani da takardar shedar firamare ta bogi.

Sai dai Zakari ya musanta amfani da takardun jabu ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, a lokacin yakin neman zabe, inda ya ce bambancin da a ka samu a cikin takardun sa na canjin suna ne, wanda aka yi bisa doka.

“Don kauce wa shakku da kuma daidaita bayanai, suna na Muktar Umar, na yi makarantar firamare ta Hausawa, na kammala a matsayin Muktar Umar.

“Vala suna na ya ke a dukkan takardun makaranta ta tun daga firamare, sakandare, da makarantun gaba da sakandire, wadanda suna nan ko da za a nemi tantancewa.

“Duk da haka, a cikin burina na ƙara sunan dangi na, sai na kara Zakari a sunana kuma na koma Mukthar Umar Zakari bayan na cika dukkan ka’idojin doka da tsarin mulki game da sauya sunayen.

Mista Umar-Zakari ya ce an yi canjin suna ne tun kafin zaben 2023.

Yayin da yake yin alkawarin mutunta doka, Mista Umar Zakari ya ce zai kalubalanci hukuncin kotun a kotun daukaka kara.

Post a Comment

0 Comments