TARIHIN FIYAYYAN HALITTA ANNABI MUHAMMAD (SAW)

 


Abdul-Muddalib ya dawo dakin Ka'aba da 'dansa Abdullahi, tare da mutanen da suka yi masa rakiya zuwa gidan tsohuwar nan mai hikima, mutuniyar Yathrib, za a yi Quri'a tsakanin Abdullahi da rakuma goma, kamar yadda tsohuwar ta bada shawara, domin in Quri'a ta fada kan rakuman, su zamo fansar Abdullahi daga yanka.

Da zuwa kuwa suka fara jefa Quri'a, Abdul-Muddalib ya roki Allah Ya ku6utar da dansa, kowa ya tsaya yana jiran ganin sakamako. Sai kuwa quri'a ta fada akan Abdullahi! Don haka sai babansa ya sake kara rakuma goma. Nan ma dai sai Quri'a ta sake fadawa kan Abdullahi, ya sake karawa, ya sake karawa, yayi ta karawa har saida aka kai rakuma dari, sannan a na darin sai aka yi sa'a kuri'a ta fada akan rakuman, Abdullahi ya ku6uta, kowa da kowa yayi matukar farin ciki da ku6utarsa.

Sai da Abdul-Muddalib ya maimaita jefa Quri'ar sau uku domin tabbatar da cewar sakamakon na gaskiya ne, amma duk in ya jefa sai ta fada akan rakuman, don haka sai yayi godiya ga Allah da Ya ku6utar da Abdullahi daga yanka.

Aka yanka dukkan rakuman nan guda dari, kuma aka girka abinci mai yawan gaske aka yi shagali saboda farin ciki, har saida abinci ya wadatar da dukkan mutanen birnin da dabbobi da tsuntsaye.

Abdullahi (AS) ya girma ya zama kyakkyawan saurayi. A lokacin nan ne mahaifinsa Abdul-Muddalib ya za6a masa wata kyakkyawar budurwa mai suna Amina 'Yar Wahbi (AS), a matsayin mata a gareshi. Hadin ya dace kwarai, domin ita ce mafi darajar mace daga matayen Qurayshawa wadda ta yi fice tsakanin mata da kyawawan dabi'u, shi kuma Abdullahi (AS) shine mafi darajar mazaje, mafificinsu a kyawawan dabi'u.

Bayan an yi auren, Abdullahi (AS) ya zauna tsawon watanni da matarsa, amma shi ma, zama a gida ba zai yiwu a gare shi ba, a matsayinsa na namiji, wajibinsa ya fita zuwa kasuwanci, kamar yadda iyaye da kakanninsa suka kasance. Saboda haka, sai ya fita tare da wani ayarin fatake zuwa Sham domin kasuwanci.

Akan hanyarsa ta dawowa Makka daga Sham din ne sai rashin lafiya ya same shi, don haka sai ya tsaya Yathrib (Madina) domin ya dan samu sauki kafin ya cigaba zuwa gida. Ayarin fataken da suke tafiya tare kuwa, sun wucewarsu zuwa Makka ba tare dashi ba.

Lokacin da suka isa Makka suka sanar da babansa Abdul-Muddalib labarin rashin lafiyarsa, sai ya tura wani daga cikin 'ya'yansa, mai suna Haris, domin ya je ya dawo dashi. Amma Kash! Ya makara, domin kafin ya je Abdullahi (AS) ya yi wafati

Amina (AS) ta yi matukar bakin cikin rasa mijinta, kuma mahaifin d'an da yake a cikinta wanda za ta haifa ba da jimawa ba. Yaron da ba a ta6a haihuwar irinsa ba kafin shi, kuma ba za a ta6a haihuwar wani tamkarsa ba a bayansa. Yaron da zai zama shiriya da rahama ga dukkan halittun duniya baki'daya, tsira da Aminci su tabbata a gashi

BY: SALISU ASUA

Post a Comment

0 Comments