Rundunar Ƴansanda ta fara bincike kan mutuwar mawaƙi Mohbad

 


Kwamishinan ƴansandan jihar Legas, Idowu Owohunwa, ya kafa wata tawaga ta musamman domin gano musabbabin mutuwar mawakin nan, Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad.


Kakakin rundunar ƴansandan, SP Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a jiya Asabar, inda ya ce an zabo tawagar ne daga ɓangaren kisan-kai na sashen binciken manyan laifuka na jihar Legas, SCID.

Ya ce tuni rundunar ta dauki matakin fara bincike kan lamarin.


Hundeyin ya ce, samar da tawagar binciken ta musamman ta zama wajibi bisa la’akari da yadda jama’a ke kara nuna damuwa da kuma cecekuce a kan mutuwar mawakin, da kuma binciken farko da ƴansanda suka yi kan al’amuran da suka shafi mutuwar.

Post a Comment

0 Comments