Matsala ce dake faruwa ga ido, wani lokacin tana shafar ido É—aya; wani lokaci kuwa za ta shafi idanuwan, idan har ido É—aya ya fara, to É—ayan shi ma nan take zai harbi É—aya.
Wannan ciwon Æ™wayar viral infection ce ke kawo shi, wani lokacin kuwa “Bacterial infection”, ya danganta da yanayin ciwon.
Kuma ciwon kan bayyana a cikin kwana biyu zuwa mako uku (days-3wks).
ALAMOMI
Wani lokacin za a ga alamomin wannan ciwon kamar haka:
-Ƙaiƙayin ido
-Kumburin ido
-Canzawar ƙwayar idanuwa
-Zubar ruwa
-Rashin son hasken rana, kowane kalar haske na daban,
-Da sauran Alamomi.
Wannan ciwon conjunctivis a kan iya É—aukar sa ta waÉ—annan hanyoyi kamar haka:
-Amfani da hankicif wanda mai wannan ciwon ke amfani da shi wurin shafe fuskarsa.
-Ko kuma gaisuwa idan mai wannan ciwon ya shafi idanuwansa.
-Da amfani da wasu hanyoyi marasa tsafta.
SHAWARA
-Tsaftace muhalli na da matuƙar muhimmanci ga lafiyar ɗan Adam
-Hana yara zuwa makaranta idan sun kamu da wannan matsalar, domin gudun wasu su kamu
-Anfani da maganin antimicrobial na mai ko na É—igawa
-Kawar da cutar ga yara musamman gonococcal_conjunctivitis
Idan kuwa abin ya yi tsanani, to sai a yi gaggawar zuwa asibiti domin ganin likita kai tsaye.



0 Comments