NECO ta Buɗe Manhajar Tabbatar da Sahihancin Sakamakon jarrabawa ta yanar gizo



Hukumar shirya jarabawar gama Sakandire ta kasa, NECO, ta kaddamar da wata manhaja mai suna “NECO ‘e-Verify” domin saukaka tantance sakamako da magudin jarrabawa da jabun sakamakon jarrabawa da hukumar  ta gudanar.

Shugaban hukumar ta NECO, Farfesa Dantani Wushishi, a jawabinsa na maraba a wajen wani taro a ranar Alhamis a Abuja, ya ce duk wasu bukatu na tantance ko tabbatar da sakamakon jarrabawa na fitowa ne daga hedkwatarsu da ke Minna, wanda ya dauki lokaci mai tsawo ana gudanar da shi.

"NECO e-Verify" hanya ce ta tabbatar sahihancin sakamakon jarrabawa ta yanar gizo da ta ke tabbatar da sahihancin sakamakon jarrabawa nan take wajen neman shiga makarantun gana da sakandare da neman aiki," in ji shi.

Wushishi ya ce saboda karuwar bukatar tantancewa da tabbatar da sakamakon da cibiyoyi na gida da waje suka yi, NECO ta yanke shawarar cewa yanzu ne lokacin da ya fi dacewa a bullo da tsarin tantancewa ta yanar gizo.

Ya yi bayanin cewa daga bayanan da ake da su, NECO ta lura cewa akwai buƙatun tantancewa da tabbatarwa kan sakamako daga cibiyoyi 64 a cikin ƙasashe 37 tsakanin 2020 da 2022.

Wushishi ya ci gaba da cewa, an samu irin wannan bukatu daga jami'o'i 72 na Najeriya a cikin lokaci guda, ya kara da cewa hakan baya ga bukatu na daidaikun mutane wadanda suke da yawa.

        MASU ALAKA DA

             NECO .               WAEC

Post a Comment

0 Comments