SAI MASU GIDA: Kano Pillars ta tafi hutun mako ɗaya bayan ta dawo gasar firimiya

  


Kwamitin rikon na Ƙungiyar Ƙwallon kafa ta Kano Pillars ya bai wa ƴan wasan kungiyar hutun mako guda bayan da suka hawo zuwa gasar Premier ta Ƙasa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ciyaman ɗin kungiyar, Babangida Umar ya fitar jim kadan bayan kammala wasan karshe na Super 8 na Najeriya a filin wasa na Stephen Keshi dake Asaba, jihar Delta.

Umar ya ce ma’aikatan ƙungiyar da ba masu buga ƙwallo ba ba za su je hutu ba har sai sun mika rahoton  kan kakar wasa ta bana.

Ciyaman ɗin kungiyar ya yabawa gwamnati da ƴan wasa dama’aikata da magoya bayan ta da kuma mutanen jihar bisa goyon bayan da suke baiwa kungiyar, wanda ya bayyana a matsayin dalilin hawowar ta gasar firimiya.

Ya yi alkawarin cewa za a samar da dukkan tallafin da ya dace domin kungiyar ta samu nasara a gasar firimiya ta bana.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa kungiyoyin kwallon kafa na Kano Pillars da Katsina United da Heartland da Sporting ne kungiyoyi hudu da suka samu damar shiga gasar Firimiyar Najeriya da ake sa ran za a fara a watan Agusta.

 MASU ALAKA DA

          WASANNI                    KANO PILLARS

Post a Comment

0 Comments