Hukumar yi wa kasa hidima (NYSC) ta ɗauke sansaninta na dindindin da ke karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau.
Yanzu haka an maida sansanin zuwa ginin WAYE FOUNDATION da ke BUKEN Academy a Doi-Du, yankin Karamar Hukumar Jos ta kudu.
Shugabar sashin hulda da jama’a na NYSC a Plateau, Ms Jennifer Laha ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar jiya a Jos.
Ta kara da cewa daga 12 ga watan Yuli ƴan bautar ƙasa na rukunin "B" na 2023 Batch “B”, zango na ll za su fara ɗaukar horo zuwa 1 ga Agusta a faɗin ƙasa.
A cewar LAHA, a ranar 14 ga watan Yuli ne za a gudanar da bikin bude sansanin da kuma rantsar da ƴan bautar ƙasa.
Laha ta ce ana sa ran gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, zai jagoranci bikin.
Ta kuma bukaci al’ummar Plateau da su yi wa ‘yan bautar ƙasa tarba mai kyau.
LABARAI MASU ALAKA DA


0 Comments