A rana mai kamar ta Yau ce, 29/10/2006 Shekaru Goma Sha bakwai (17) Cif da Jirgin Kamfanin ADC Airline yayi hatsari Jim kadan bayan tasowar sa daga Filin Jirgin Sama Na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, kan hanyar sa ta zuwa Sokoto.
Hatsarin Jirgin wanda yayi Sanadiyyar Kashe Mutane fiye da 100 Musamman Jiga-jigan 'Yan Jihar Sakkwato.
Daga cikin Wadanda suka rasa ransu 'yan jihar Sakkwato akwai
1. Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido.
2. Alh. Garba Muhammad Silame, Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato.
3. Sanata Badamasi Maccido
Sokoto Central.
4. Sanata Sule Yarin Gandi, Sokoto East
da wasu Iyalansa.
5. Dr. Sanusi Usman Junaidu
Kwamishinan Ilimi Na Jihar Sakkwato.
6. Alh. Uwaisu Yaro Bodinga
7. Hon. Abdulrahman Shehu Shagari.
Dan takarar kujerar Reps Yabo/Shagari
8. Alh. Bello Kware
9. Alh Babuga Dange Secretary to Sultana Council
Da Sauran Al'umma.
Tabbas Al'ummar Jihar Sakkwato da Kasa baki daya ba zasu taba mantawa da wannan Ranar ba a tarihi.
Muna Fatar Allah SWT ya kara Jaddada Rahamarsa da Jin kansa a gare su da sauran al'ummar da suka riga mu gidan Gaskiya, ya kaddari Aljannar Fiddausi ta kasance makoma agare mu baki daya don darajar Alkur'ani Maigirma 👏👏👏

0 Comments