Amfanin magani, shi ne ya warkar da cuta, ko ya rage ta, ko ya hana kamuwa da ita.
Asalin dukkan magunguna, yana kasancewa daga tsire-tsire ko daga abubuwa da aka tono daga kasa, ko kuma daga abubuwa da ake samu daga jikin dabbobi da kuma waÉ—anda masu ilmin kimiyya suke zama, su harhad'a da kansu, a É—akinsu na kimiyya.
Likita in ya ba da magani, yana bayarwa gwargwadon bukatar jikinka ne. Ba ya ba ka wanda zai yi karanci, yadda ba zai yi amfanin da ake bukata ba. Kuma ba zai ba ka da yawa yadda jikinka zai kasa dauka ba.
Babba yana bukatar magani da ya fi yawan wanda za a bai wa yaro Haka kuma mutum mai tsamurarren jiki, ba zai bukaci magani da yawa kamar katon mutum mai jiki ba. Karfin cuta shi ma, yana nuni ga yawan magani da ya kamata a bai wa maras lafiya.
In an ba da wasu magunguna, dole a lura ko za su iya jawo wata Barna ta bazata ga yadda jiki yake aiki, su jawo lahani. Misali, akwai wata irin allura da take da amfani wajen kashe kwayoyin cuta. In ba a yi sa'a ba, sai ta jawo wanda aka yi wa allurar ya fadi warwar, num- fashinsa ya É—auke, har in aka hadu da hatsari sosai sai mutuwa Wasu kuma sai su sa kuraje su fito birjik, duk jikin mutum.
Bayan wannan kuma, magunguna da yawa suna jawo abin da ba a so ga jikì, bayan aikinsu na amfani. Irin wadannan aibace-aibace na magunguna, su suka sa masu ilmin kimiyya suke ta gwada magunguna ta hanyoyi da yawa don a tabbata ba za su jawo wani abin ki ba ga yadda jikinmu yake aiki, kafin a bari jama'a su fara amfani da Su.
Ta hanyoyi hudu ake amfani da magani :-
1 sha da
2 shafawa da
3 Allura da
4 shaka.
Ga misalin wadannan hanyoyi na amfani da magani:
1
a) kwayoyi
b) ruwan magani
c) kafso
d) hodar magani.
2
a) masu kama da mai
b) lilimanti
c) masu kama da ruwan hoda
d) masu kama da kwantsa
e) wanda aké ɗauke da su.
3
a) maganida launinsa garai kamar ruwa
b) maganida launinsa ya sake.watau yayi wani launi Kala..
Ana allura a cikin tsokar jiki ko cikin fata ko cikin hanyar jini ko cikin gaba.
4
Yawanci, an fi amfani da wadannan, ga masu cuta mai shake numfashi.
Da an shaka, nan da nan sai a yi numfashi cikin sauki.
:
Yawan amfani da wadansu daga irin v. ad annan magunguna, na iya lahani ga zuciya.
an Zamu diga Aya Acikin Wannan Topic Na Ilimin Cututuka Na jikin Dan Adam….. Sai Mu hadu A Kashi na biyu…..Domin Dorawa inda Muka tsaya……

0 Comments