Zaɓen sanatan Kano-ta-Tsakiya: Tirabunal ta yi watsi da ƙarar AA Zaura a kan Rufa’i Hanga



Kotun sauraren ƙararrakin zaben Majalisar Tarayya da ta Dokokin Jihar Kano, ta yi watsi da ƙarar da Abdussalam Abdulkarim Zaura na jam’iyyar APC ya shigar, da ke kalubalantar zaben Rufa’i Sani Hanga a matsayin Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya.

Mai shigar da karar ya shigar da karar ne domin kalubalantar nasarar Sani Hanga na jam’iyyar NNPP, a zaben Sanatan Kano ta tsakiya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Wadanda Zaura ke ƙarar sun haɗa da INEC, NNPP, Rufa’i Sani-Hanga da Ibrahim Shekarau.

Yayin zartar da hukuncin, kwamitin mutum uku na Tirabunal, karkashin jagorancin Mai shari’a I P Chima, ya ce wanda ya shigar da karar ya kasa gamsar da kotun a bisa doron dokar zaɓe ta 2022.

“Zaben Sani-Hanga ta tabbatacce ne kuma an kori karar”

Alkalin ya kuma umurci wanda ya shigar da karar ya biya NNPP Naira dubu 300 sannan ya biya Sani-Hanga Naira dubu 300 sakamakon ɓata musu lokacin da 6a yi a kotun.

Post a Comment

0 Comments