NDLEA ta cafke lauya mace tare da wasu mutane ɗauke da miyagun ƙwayoyi

 


Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta kama wata lauya mai suna Ebikpolade Helen, wacce ta kware wajen hadawa da rarraba skuchies, da cakuda wiwi, da wasu miyagun kwayoyi.

A wata sanarwa da kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ta ce matar tana zaune ne a unguwar Lekki da ke jihar Legas.

Babafemi ya ce an kama wadda ake zargin ne a wani sumame da aka kai garin Awka a jihar Anambra, biyo bayan kama tabar wiwi mai nauyin kilogiram 5 da kwalabe 12 da aka boye a bayan gidanta da ke Lekki.

Ya kuma ce an kama wani wanda ake zargin Abubakar Shuaibu a ranar 13 ga watan Yuli a Cappa, da ke titin Mushin-Oshodi dauke da kwalabe 86 na maganin tari na kodin.

Mista Babafemi ya ce magungunan da nauyinsu ya kai lita 8.6 suna cikin motar sa ta Toyota mai lamba FFA 241YB.

Post a Comment

0 Comments