Tinubu ya naɗa mashawarta a ɓangarori daban-daban


 Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa masu ba shi shawara kan harkoki daban-daban ciki har da Mallam Nuhu Ribaɗu a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro na musamman.

Wata sanarwa da Abiodun Oladunjoye, daraktan yaɗa labarai a fadar shugaban Najeriya ya fitar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da naɗe-naɗen da suka haɗar da Mista Dele Alake a matsayin mai ba da shawara kan harkar ayyuka na musamman, sadarwa da tsare-tsare.

Akwai kuma Mallam Ya'u Darazo a muƙamin mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa da hulɗa tsakanin gwamnatoci.

                                                                 TALLA

Haka zalika, Tinubu ya amince da naɗa Mista Wale Edun a matsayin mai ba da shawara na musamman kan manufofin kuɗi. Akwai kuma mai ba da shawara ta musamman kan harkokin makamashi, inda Tinubu ya naɗa Misis Olu Verheijen. 

Ƙarin masu bayar da shawarar har da Mista Zachaeus Adedeji a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin kuɗin shiga. An kuma naɗa Dr. Salma Ibrahim Anas a muƙamin mai ba da shawara ta musamman a fannin kula da lafiya.

                                                               TALLA

Sai kuma Mista John Ugochukwu wanda aka naɗa mai ba da shawara na musamman kan harkokin masana'antu, kasuwanci da zuba jari

Post a Comment

0 Comments