Ranar dimokuraɗiyya: Gwamnan jihar Neja ya yafewa ɗaurarru 80



Gwamna Umaru Bago na Jihar Neja ya yi afuwa ga wasu fursunoni 80 da ke gidajen gyaran hali daban-daban a jihar.

Gwamnan ya kuma amince da biyan tarar da aka yi musu cikin gaggawa, domin baiwa fursunonin damar komawa cikin iyalansu.

A wata sanarwa da Abubakar Usman, sakataren gwamnatin jihar, SSG, ya fitar a Minna a yau Litinin, ya ce an gudanar da afuwar ne domin murnar zagayowar ranar dimokuradiyya ta 2023.

Ya bayyana cewa sakin fursunonin ya yi daidai da ikon jinkai da tsarin mulki ya baiwa gwamna.

Usman ya ce majalisar ba da shawara kan jinkai ta jihar ce ta ba da shawarar a saki fursunonin 80 saboda tsufa, rashin lafiya da kuma kyawawan halaye.

Usman ya yi kira ga fursunonin da su yi amfani da damar da suke da su wajen yin sana’o’i masu amfani tare da yin watsi da duk wani abu da zai kai su ga komawa gidan yari.

Ya kuma gargaɗe su da su kasance masu bin doka da oda da gudanar da ayyukan da suka dace ta hanyar amfani da tagogi daban-daban na karfafawa.

Post a Comment

0 Comments