Mutane 27 Sun Mutum Bayan Da Kwale-kwalen ƴan ci-rani ya kife a Tunisia

 Mutane 27 Sun Mutum Bayan Da Kwale-kwalen ƴan ci-rani ya kife a Tunisia 

Mutum 27 ne suka mutu yayin da wasu kwale-kwalen ƴan  ci-rani suka nutse a gaɓar tekun Tunisia. BBC ya rawaito cewa Kwale-kwalen farko ya bar Tunisia ne a ranar Juma'a inda ya nufi Italiya ɗauke da mutum 37.

Mutum 20 sun bata yayin da aka ceto wasu 17 na daban, in ji kakakin kotun birnin Sfax. A ranar Asabar, an gano gawarwaki huɗu a bakin ruwa bayan kwale-kwale na biyu ya nutse.

An ceto mutum 36 a kwale-kwale na biyu, a cewar kakakin mutum uku na daban sun ɓata. Kakakin Faouz Masmoudi ya ce duka kwalekwalen na roba ne.

Tun farkon watan Maris an samu nutsewar jiragen 'yan cirani bakwai a wannan gaɓar kogin. Wata gaɓar tekun a Tunisia ba ta fi nisan kilomita 150 zuwa Lampedus ba, wani tsuburi a Italiy, wanda duk wanda ya isa nan ana masa kallon yana cikin Italiya.


            #TUNUSIA.                  #LABARAN KASA

Post a Comment

0 Comments