Ganduje ya Kafa kwamitin Miƙa Mulki Mai Mambobi 17
Majalisar zartaswa ta Jihar Kano ta amince da kafa kwamitin mika mulki na mambobi 17 ga gwamnati mai jiran gado a jihar. Majalisar ta kuma amince da wani karamin kwamiti mai mutum 100 wanda za a fitar da kundin tsarin mulki daga ma’aikatu da hukumomi daban-daban a jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa a yau Lahadi.
Ya ce kwamitin wanda ke karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jiha, Alhaji Usman Alhaji yana da wadannan mambobi a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnati, babban lauya/kwamishanan shari’a, kwamishinan yada labarai, kwamishinan muhalli, kwamishinan kasuwanci.
Sauran sun hada da kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi, kwamishinan kananan hukumomi, kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa, kw amishinan kudi, kwamishinan ilimi da sauransu. Malam Garba ya bayyana cewa, babban kwamatin zai yi aiki cikin kwazo da nufin mika mulki cikin makonni uku.
Kwamishinan ya bayyana cewa an bai wa babban kwamitin na wucin-gadi umarnin fara shirin mika mulki tare da rubuta nasarorin da aka samu a cikin wa’adin mulki biyu na gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.


0 Comments