An Kama Mutane 40 Bisa Zargin Tayar da Tarzoma A Lokacin Zaben Gwamna A Zamfara

  


Rundunar ƴan sanda a jihar Zamfara ta ce ta kama ɓata-gari 40 waɗanda ake zargi sun mayar da murnar cin zabe zuwa tarzoma, wanda ya janyo lalata da kuma satar kayayyakin gwamnati a ofisoshin jam'iyyar APC da kuma gidajen mutane wadanda yawanci ƴan siyasa ne.

A cikin wata sanarwa da Æ´an sanda a jihar suka fitar ta hannun kakakinsu SP Mohammed Shehu, ta ce kwamishinan Æ´an sandan jihar CP Kolo, tare da haÉ—in-gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun yi kokari wajen shawo kan al'amura, inda bayan nan suka kama mutum 26 waÉ—anda ake zargi da hannu a lamarin.

Sanarwar ta kuma ce binciken da ƴan sanda ke ci gaba da yi, ya sanya sun kama ƙarin mutum 14 da kuma ƙwato kayayyaki da ɓata-garin suka sace.

Kwamishinan Æ´an sandan ya yi kira da a kwantar da hankali, inda ya tabbatar da cewa suna bincike da nufin kamo waÉ—anda ake zargin sun tsere da kuma masu taimaka musu domin ganin an hukuntasu.

Post a Comment

0 Comments