TARIHIN GIDAN MAKAMA DA KE BIRNIN JIHAR KANO,

 


An gina gidan ne a Æ™arni na Goma Sha Biyar zamanin Sarkin Kano Abdullahi Barja, ya gina gidan saboda jikansa Muhammad Rumfa wanda aka naÉ—a Makaman Kano, Daga baya Rumfa ya zama Sarki ya koma sabuwar Fadar da ya gina ta (Ƙofar kudu Gidan Sarki Na Yanzu) Bayan da Turawan mulkin mallaka suka Æ™wace Kano a shekarar Alif da ÆŠari Tara da Uku (1903), sai suka mayar da wurin ya zama ofishin jami’an mulkin mallaka na Kano a taÆ™aice. Daga baya aka raba tsarin zuwa sassa uku.

Wani sashe ya zama gidan kayan gargajiya da sashen kayan tarihi ke gudanarwa, wani kuma ya zama makarantar firamare kuma na uku aka mayar da shi ainihin manufar ginin Gidan zama.

Gidan Makama yanzu ya na cikin gidajen tarihi da ke Æ™arÆ™ashin kulawar hukumar kula da gidajen Al’adu da tarihi ta Æ™asa kuma É—aya daga cikin tsoffin gine-ginen da ke nuna gine-ginen Æ™asar Hausa.

Asalin ginin ya na ƙunshe da bangon laka irin na zamanin Da, amma a shekarun baya an yi aikin gyare-gyare na zamani.

Gidan Makama shi ne wajen ajiye kayan tarihi a Kano, an kuma gina shi tun ƙarni na Goma Sha Biyar zamanin mulkin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa, a matsayin gidan sarki na wancan lokacin.

A shekarun Alif da ÆŠari Tara da Saba’in (1970) ne aka gano wasu manyan tukwane a Æ™arÆ™ashin Æ™asa lokacin da ake gina titin Kabuga.

Masu haƙo kayan tarihi a wancan lokaci sun ce, waɗannan tukwane za su kai shekaru Ɗari Biyar a ƙasa. Ana zaton mutanen Kano na wancan lokaci kan yi amfani da su ko dai don ajiyar ruwa ko kayan amfanin gona.

Akwai kayan tarihi da dama da Turawan Mulkin mallaka suka tafi da su Ingila a wancan lokaci. Daga cikinsu akwai ƙofar ita kanta, ta shiga gidan Makaman da sauran abubuwa masu muhimmanci.

Bayan kayan tarihi da ke ajiye a gidan Makama, akwai gine-gine da aka yi a cikin gidan da ke nuna al’adu na mutanen da. Misali, an gina wani É—aki da aka yi jere na tasoshi da gadon bono, wanda ke nuni da yadda ake shirya É—akin amarya a wancan zamani. 

           TARIHI .                     AL'ADUN HAUSA

Post a Comment

0 Comments