Real Madrid da Juventus na son Richarlison, Mbappe ya yi nadamar ƙin barin PSG

 



Dan wasan gaba a Tottenham da Brazil Richarlison, mai shekara 25, ya shiga cikin jeren 'yan wasa irinsu, Kylian Mbappe na Paris St-Germain da Faransa mai shekara 24, da Gonçalo Ramos na Benfica da Portugal, mai shekara 21, a matsayin wanda ake son su maye gurbin ɗan wasan Faransa Karim Benzema, mai shekara 35, a Real Madrid. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Juventus na kuma son ganin ta dauko Richarlison domin ya maye gurbin dan wasanta na Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 23, da ake sa rai zai bar kungiyar ta Serie A, a wannan kaka. (Calciomercato - in Italian)

Mbappe ya tuntubi Real Madrid a kakar da ta gabata – ta wakilansa – inda ya ce ya yi nadamar sabunta kwantiraginsa da PSG tare da bukatar kungiyar ta La Liga ta dauke shi. (Marca)

Real Madrid na son Mbappe, amma kuma fatansu shi ne su cimma yarjejeniya da shi idan kwantiraginsa na PSG ya kare a 2024.

Dan wasan Tottenham kuma kyeftin a Ingila Harry Kane, mai shekara 29, ya kasance wanda Manchester United ke hari a wannan kaka.

Amma dai Tottenham, a shirye su ke su bai wa Kane fifiko kan makomar kulob din inda suke kokarin ganin sun shawo kan sa, ya tsawaita zama da su bayan kwantiraginsa mai karewa a 2024.(90min)

Mai buga tsakiya a Manchester City da Jamus Ilkay Gundogan, dan shekara 32, ya kasance cikin 'yan wasan da Barcelona ke hari a wannan kaka. (Sport - in Spanish)

Post a Comment

0 Comments