CANJE CANJEN MUKAMAI BAYAN SAMUN MULKIN KAI A NIGERIA

 CANJE CANJEN MUKAMAI BAYAN SAMUN MULKIN KAI A NIGERIA



Tun daga 1914 da aka hada kasar kudu da ta arewa aka kira ta nigeria had ya zuwa 1939 kafin yakin duniya na biyu, haka  wannan kasa take. A shekara ta 1939 an sake raba kudancin nigeriya in da aka yi jihar gabas data yamma. Yayin da aka fara tsarin majalisa a sabon tsarin mulki na 1947, aka shigo da harkokin siyasa. 

Saboda wayewar "yan kudancin kasar nan akan na arewa, wannan tasa sun riga 'yan arewa ba su fara kafa jam'iya ba sai a 1951. A shekarar 1954 an yi  zaban farko kan siyasa, amma kowanne ya kebanta da jiharsu.

A shekarar 1955 domin ingantuwar aiki, gwamnatin arewa ta kafa hukumar daukar ma'aikata ta farko. Wannan hukuma ta yi taronta na farko  1/2/1955 a garin kaduna. Malam bello kano ne kadai dan kasa bakar fata da ya fara shiga wannan hukuma a matsayin wakili. Wannan mukami ya rike har ya zuwa 1960.

Bayan samun mulkin kai an kafa sabuwar hukumar daukar ma'aikata ta arewa inda aka nada Alhaji Abubakar imam a matsayin shugaba, an kuma nada Makama Malam Bello Kano a matsayin kwamishina da Alhaji Abba Gusau shi ma kwamishina ,da Malam A.A babagana kuma sakataran hukuma. A wannan aiki ne har a 1961 suka yi tafiya kasashen waje domin daukar kwararrun ma'aikatan da zasu yi wa arewa kafin 'yan arewa su goge. Makaman kano Bello  Kano ya ci gaba da wannan aiki har ya zuwa lokacin juyin mulkin aka raba kasar zuwa jahohi goma sha bibiyu 12.

Post a Comment

0 Comments